Barca ba za ta sayar da Neymar ba

Image caption Neymar ya ci kofunan La Liga da Copa del Rey a Barcelona a bana

Barcelona ba ta tunanin sayar da Neymar ga kowacce kungiya, in ji mataimakiyar mai kula da harkokin kudin kulob din Susana Monje.

A cikin watan Yunin 2018 yarjejeniyar Neymar za ta kare a Barcelona, kuma tuni kungiyar ta fara tattaunawa da shi domin ta tsawaita zamansa.

Paris St-Germain, wadda daya ce daga cikin kungiyoyin da ake alakanta cewar za su dauki Neymar, ta ce za ta ninka masa albashinsa.

Neymar ya ci kwallaye 31 a wasanni 49 da ya buga wa Barcelona a kakar da aka kammala.

Dan wasan ya kuma dauki kofin La Liga da na Copa del Rey, yayin da kungiyar tasa ta kai wasan daf da na kusa da karshe a gasar zakarun Turai.

A cikin watan Yuni aka tilasta wa Barca biyan fan miliyan hudu da dubu dari uku, saboda kuskuren da aka yi wajen sayo dan wasa daga Santos a shekarar 2013.