Ko kun san wasannin hamayyar Premier bana?

Image caption Mourinho ya dauki kofunan Premier uku a Chelsea

Za a fara buga gasar Premier bana a ranar 13 ga watan Agusta, kamar yadda aka fitar da jadawali.

Arsenal za ta fafata da Liverpool a wasan farko na gasar ta bana a filin wasa na Emirates a ranar.

Mai rike da kambun gasar Leicester City za ta ziyarci Hull City.

A gasar ta bana da akwai wasannin hamayya a za a yi da dama.

Daga cikinsu har da fafata tsakanin Jose Mourinho da Pep Guardiola, inda Man United da Man City za su kece-raini a Old Trafford a ranar 10 ga Satumba.

Haka kuma Mourinho din zai kara da Chelsea wadda ya dauki kofuna uku a kungiyar karo biyu a gasar.

Sabon kocin Everton, Ronald Koeman, zai karbi bakuncin tsohuwar kungiyarsa Southampton a ranar 26 ga watan Nuwamba.

Sannan ya ziyarci Goodison Park a ranar 2 ga watan Janairun 2017.

Shi kuwa Eddie Howe mai horar da Bournemouth zai kara da tsohuwar kungiyar da ya jagoranta Burnley a ranar 10 ga watan Disamba.

Su kuma kara a wasa na biyu a cikin watan na Disambar.

Ga jerin wasannin hamayya a gasar Premier bana.
 • 10/9: Man Utd v Man City
 • 25/2: Man City v Man Utd
 • 5/11: Arsenal v Tottenham
 • 29/4: Tottenham v Arsenal
 • 17/12: Everton v Liverpool
 • 1/4: Liverpool v Everton
 • 20/8: Sunderland v Middlesbrough
 • 11/3: Middlesbrough v Sunderland
 • 17/12: Bournemouth v Southampton
 • 1/4: Southampton v Bournemouth
 • 24/9: Arsenal v Chelsea
 • 4/2: Chelsea v Arsenal
 • 19/11: Tottenham v West Ham
 • 6/5: West Ham v Tottenham