Lionel Messi ya sake kafa tarihi

Image caption Ana zargin Messi da zillewa biyan haraji

Lionel Messi ya zama dan kwallon kafar da ya fi cin kwallaye a kasarsa, bayan da ya ci kwallo a wasan da Argentina ta doke Amurka da ci 4-0 inda ta kai zagayen karshe na cin kofin Copa America.

Dan wasan gaban na Barcelona, mai shekarar 28, ya zarta Gabriel Batistuta, wanda ya ci kwallaye 54.

Messi ne ya mika wa Ezequiel Lavezzi kwallon da ya fara bude fage da ita, sannan ya zura tasa kwallon, yayin da dan wasan Napoli, Gonzalo Higuain ya zura kwallo ta uku.

Higuain ya kara zura kwallo a minta na 85, inda aka tashi 4-0.

Messi ya ce,"Ina matukar farin ciki da na zarta Batistuta a wajen zura kwallaye, sannan ina mika godiya ta ga abokan wasa na. Wannan nasara ce a gare su su ma."

Argentina za ta fafata da ko dai Colombia ko kuma Chile a wasan karshe ranar Lahadi.

A ranar Juma'a ne dan wasan zai cika shekara 29 a duniya.