Manchester City na son sayen Nolito

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Nolito yana buga wa tawagar Spaniya gasar Turai da ake yi a Faransa

Manchester City na son ta sayi dan kwallon Celta Vigo, Nolito, domin ya buga mata tamaula a bana.

Nolito zai iya barin Celta Vigo idan aka biya fam miliyan 13 da dubu dari takwas, kuma sai a shekarar 2018 ne yarjejeniyarsa za ta kare.

Dan wasan mai shekara 29, wanda ke buga gasar Turai ta bana, wanda Barcelona ma ke zawarci bai yanke shawara ba zuwa yanzu.

Nolito dan Spaniya, ya fara wasa a Barcelona, a shekarar 2010 karkashin Pep Guardiola.

Daga nan ne ya koma Benfica a shekarar 2011, sannan ya je Celta da murza-leda.

Idan har ya koma City zai zama dan kwallo na biyu da ta saya a bana, bayan Ilkay Gundogan da aka sayo daga Borussia Dortmund.