Togo ba za ta sallami LeRoy daga aiki ba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kociyan ya horar da tamaula a kasashe da dama a Afirka

Hukumar kwallon kafa ta Togo, ta ce ba zata sallami kocinta Claude LeRoy ba, duk da masu shigar da karar Faransa na kira a dauke shi.

LeRoy na fuskantar tuhuma kan hannu da yake da shi a badakalar sayar da 'yan wasan Racing Club de Strasbourg a shekarar 1990 da 2000.

Masu shigar da kara a Faransa sun bukaci babbar kotun Strasbourg ta daure LeRoy shekara biyu.

Kociyan ya shaidawa BBC cewar tun a baya a saninsa ya wanke kansa dangane da zargin da ake yi masa.

LeRoy ya fara jan ragamar tawagar Togo tun a cikin watan Afirilu, inda ya maye gurbin Tom Saintfiet.

Kociyan ya horar da kungiyoyi da dama a Afirka ciki har da Ghana da Senegal da Jamhuriyar Congo, ya kuma lashe kofin nahiyar Afirka da Kamaru a shekarar 1988.