Ronaldo ya ci kwallaye a gasar Turai hudu

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ronaldo ya buga gasar Turai ta 2004 da 2008 da 2012 da kuma ta 2016 da ake yi a Faransa

Cristiano Ronaldo ya kafa tarihin cin kwallo a gasa hudu ta cin kofin nahiyar Turai da ya buga a jere.

Dan wasan na tawagar Portugal ya fara buga wa kasar gasar nahiyar Turai ne a shekarar 2004, ya kuma ci kwallaye biyu a wancan lokacin.

A gasar da aka buga ta 2008 kuma kwallo daya kacal ya ci, yayin da ya zura guda uku a raga a gasar da aka yi a shekarar 2012.

A gasar da ake yi ta bana a Faransa, Ronaldo ya ci kwallo biyu a karawar da suka tashi 3-3 da Hungary a ranar Laraba.

Jimillar kwallaye takwas ke nan dan wasan ya ci a gasar hudu, kuma saura kwallo daya ya yi kan-kan-kan da Michel Platini, wanda ya ci tara a tirihin gasar.