Elmohamady zai ci gaba da wasa a Hull

Hakkin mallakar hoto Reax Features
Image caption Dan wasan tawagar Masar, tsohon dan kwallon Sunderland

Ahmed Elmohamady ya sanya hannu a kan yarjejeniyar shekara uku domin ci gaba da buga wa Hull City tamaula.

Elmohamady, dan wasan tawagar Masar, ya koma Hull City da murza-leda a matsayin aro daga Sunderland a shekarar 2012.

A shekarar 2013 ne Hull City ta sayi dan wasan kan kudi fan miliyan biyu.

Dan wasan mai shekara 28 ya yi wa Hull wasanni 51 a bara, inda ya taimakawa kungiyar samun tikitin buga gasar Premier bana.

Hull City za ta karbi bakuncin Leicester City wadda ke rike da kofin Premier a ranar 13 ga watan Agusta.