Tottenham ta dauki Victor Wanyama

Image caption Zai sake yin wasa karkashin Mauricio Pochettino wanda ya horar da shi a Southampton

Tottenham ta kammala sayen dan kwallon Southampton, Victor Wanyama, mai buga wa tawagar Kenya tamaula.

A ranar Litinin BBC ta ruwaito cewar Tottenham za ta dauki Wanyama kan kudi fan miliyan 11.

Tuni kuma dan kwallon, ya saka hannu a yarjejeniyar zai buga wasanni a White Hart Lane shekara biyar.

Dan wasan mai shekara 24 ya koma Southampton da murza-leda kan kudi fan miliyan 12 da dubu 500 a shekarar 2013.

Wanyama wanda ya buga wa Southampton wasannin League sau 85 ya kuma ci kwallaye hudu, zai taka leda a karkashin koci Mauricio Pochettino wanda ya horar da shi a Southampton.