Liverpool za ta sayi Sadio Mane

Hakkin mallakar hoto getty
Image caption Mane yana burge Klopp

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool na son sayen dan wasan Southampton Sadio Mane a kan £30m.

Kocin kungiyar Jurgen Klopp yana so ya kara wa masu cin kwallo karfi kuma a shirye yake ya sayi Mane ko nawa zai kashe.

Liverpool da Southampton za su ci gaba da tattaunawa a kan sayen dan wasan mai shekara 24.

Da alama kungiyar ta Southampton za ta nemi Liverpool ta biya ta £40m domin sayen dan wasan, wanda ya zura kwallaye 11 a wasannin Premier 37 da ya buga a kakar wasan da ta wuce.

Sai dai watakila za a jinkirta sayen Mane ganin cewa Southampton ba ta da koci a yanzu komawar Ronald Koeman Everton.

Mane yana burge Klopp, wanda aka yi tsammanin zai koma Manchester United lokacin Louis van Gaal yana kocin kungiyar.