Algeria ta nada Rajevac sabon kociyanta

Hakkin mallakar hoto cleve mason getty
Image caption Milovan Rajevac na fatan kai Algeria gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a 2018

Hukumar kwallon kafa ta Algeria ta sanar da nada Milovan Rajevac, a matsayin sabon kociyan tawagar kwallon kafarta.

Rajevac mai shekara 62, zai maye gurbin Christian Gourcuff, wanda ya ajiye aikin a cikin watan Afirilu.

Kocin ya taba horar da tawagar kwallon kafa ta Ghana, inda ya kai ta wasan daf da karshe a gasar kofin duniya ta 2010 da aka yi a Afirka ta Kudu.

Rajevac dan kasar Serbia ya kuma horar da tawagar kwallon kafar Qatar a baya.

Algeria tana rukuni na biyu da ya kunshi Nigeria da Kamaru da kuma Zambia a wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da za su fara karawa a cikin watan Oktoba.