Faransa za ta kara da Ingila ko Iceland

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Faransa za ta kara da Ingila ko kuma Iceland a wasan daf da na kusa da karshe

Mai masaukin baki Faransa a gasar cin kofin nahiyar Turai ta kai wasan daf da na kusa da karshe, bayan da ta ci Jamhuriyar Ireland 2-1 a ranar Lahadi.

Jamhuriyar Ireland ce ta fara cin kwallo ta hannun Robbie Brady minti biyu da fara tamaula, bayan da aka yi wa Shane Long keta a da'ira ta 18.

Faransa ta farke kwallon ta hannun Antoine Griezmann, minti 12 da dawowa daga hutu, kuma shi ne dai ya kara ta biyu.

Jamhuriyar Ireland ta kammala karawar da 'yan wasa 10 a cikin fili, bayan da aka kori Shane Duffy.

Faransa za ta kara da wadda ta yi nasara tsakanin Ingila ko kuma Iceland a ranar 3 ga watan Yuli.