Euro 2016: Roy Hodgson ya yi murabus

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Shekarar Roy Hodgson 4 yana horas da kungiyar ta Ingila.

Kociyan kungiyar wasan kwallo ta Ingila, Roy Hodgson ya yi murabus, bayan da Iceland ta doke kungiyar tasa daga gasar da ci 2-1.

Kociyan mai shekara 68 dai ya kwashe shekara hudu yana horas da kungiyar, tun bayan da ya maye gurbin dan Italiyar nan Fabio Capello.

Roy ya ce " ku yi hakuri, dole haka abin ya kasance amma dai hakan na faruwa."

Wasu dai na dauka cewa kungiyar wasa ta Iceland din wanda na daya daga cikin kungiyoyin wasan da aka raina a gasar ta Euro 2016, ta kunyata Ingila.