An fitar da Spaniya daga gasar nahiyar Turai

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Italiya za ta kara da Jamus a wasan daf da na kusa da karshe

Italiya ta fitar da Spaniya mai rike da kofin nahiyar Turai daga gasar bana da ake yi a Faransa.

Italiya ta doke Spaniya ne da ci biyu da babu ko daya, kuma Giorgio Chiellini da Graziano Pelle ne suka ci mata kwallayen.

Da wannan sakamakon ne, Italiya wadda ta kai wasan daf da na kusa da karshe za ta kara da Jamus a ranar Asabar.

Spain ta dauki kofin nahiyar Turai a shekarar 1964 da 2008 da kuma 2012, yayin da Italiya ta dauka a shekarar 1968.