Juventus na gwajin lafiyar Alves

Image caption Dani Alves ya yi shekara takwas a Barcelona

Likitocin kungiyar Juventus na gwajin lafiyar Dani Alves, kafin ta kulla yarjejeniyar daukar dan wasan daga Barcelona.

Alves mai shekara 33, ya dauki kofin zakarun Turai uku da na La Liga shida da Copa del Rey hudu a shekara takwas da ya yi a Barcelona.

Wasu rahotanni na cewar dan wasan na tawagar Brazil, zai saka hannu kan yarjejeniyar shekara biyu.

Tun a farkon watan nan Juventus ta dauki dan kwallon Roma, Miralem Pjanic.