Za a fitar da jadawalin La Liga a watan Yuni

A cikin watan Agustan 2016 za a fara wasannin La Liga

Asalin hoton, epa

Bayanan hoto,

A cikin watan Agustan 2016 za a fara wasannin La Liga

Ana sa ran za a fitar da jadawalin fara gasar La Liga ta Spaniya ta kakar bana 2016/17 a ranar 21 ga watan Yuli.

Ana kuma sa ran za a fara wasannin bana ne a ranar 21 ga watan Agustan 2016.

Barcelona ce ta dauki kofin La Ligar da aka kammala, kuma na 24 da ta lashe jumulla a tarihin gasar.

Sabbin kungiyoyi uku da suka samu gurbin buga gasar La Liga sun hada da Deportivo Alavés da CD Leganés da kuma CA Osasuna.

Wadanda suka bar gasar da aka gama sun hada da Rayo Vallecano da Getafe da Levente.

Ana sa ran kammala wasannin La Ligar bana a ranar 13 zuwa 14 ga watan Mayun 2017.