Blanc ya ajiye aikin horar da PSG

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sau uku a jere PSG tana lashe kofin kasar Faransa

Lauren Blanc ya ajiye aikin horar da Paris St-Germain, bayan da ya jagoranci kungiyar shekara uku.

Blanc wanda ya tsawaita yarjejeniyar ci gaba da horar da PSG a cikin watan Fabrairu, ya lashe kofin kasar Faransa sau uku.

Sai dai kuma sau uku PSG tana fita daga gasar cin kofin zakarun Turai a wasan daf da na kusa da karshe, karkashin jogorancinsa.

Ana rade-radin cewar kociyan Sevilla, Umai Emery, ne zai maye gurbinsa.

Emery ya lashe kofin zakarun Turai na Europa League sau uku tare da Sevilla.

Tun a farkon watan nan shugaban PSG, Nasser Al-Khelaifi, ya sanar da cewar za a yi sauye-sauye a kungiyar.