Ana gwada lafiyar Mane a Liverpool

Hakkin mallakar hoto Rex Features
Image caption Southampton na son ta sayar da Mane kan kudi fan miliyan 40

Dan kwallon Southampton, Sadio Mane ya ziyarci Anfield, domin a gwada lafiyarsa, kan shirin komawa Liverpool da taka-leda.

Ana cewar Mane, zai saka hannu kan yarjejeniya kudi fan miliyan 34, watakila kudin ya kai fan miliyan 36, wanda hakan zai zama dan wasa mafi tsada da zai murza-leda a Liverpool.

Sai dai kuma Southampton na neman Liverpool ta biya fan miliyan 40, kudin dan kwallon.

A ranar Talata ake sa ran za a kammala ciniki tsakanin kungiyoyin biyu.