Djokovic zai kare kambunsa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Novak Djokovic zai kare kambunsa

A ranar Litinin ne zakaran wasan Wimbledon Novak Djokovic zai kare kambunsa a gasar da za a fara.

Dan wasan zai fafata da James Ward a Centre Court da ke Biritaniya da misalin karfe daya na rana.

A ranar ta Litinin ne kuma mutumin da ya sau bakwai yana zama zakaran Wimbledon Roger Federer da Garbine Muguruza za su yi tasu fafatawar.

Andy Murray da Johanna Konta za su fara nasu wasan ranar Talata.