Bai kamata Messi ya yi ritaya ba - Maradona

Messi ya samu nasarori a kungiyar kwallon kafa ta Barcelona

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Messi ya samu nasarori a kungiyar kwallon kafa ta Barcelona

Shugaban kasar Argentina da Diego Maradona sun yi kira ga Lionel Messi da ya janye batun ritayar da ya yi daga buga wa kasar tamaula.

Messi mai shekara 29, ya yi murabus daga buga wa Argentina wasanni ne, bayan da Chile ta doke kasarsa a bugun fenariti, kuma Messi yana daga cikin 'yan wasan da suka barar da kwallo.

Rashin nasarar da Argentina ta yi da Chile, shi ne na hudu da kasar ta kasa cin wasan karshe.

Maradona ya fada wa jaridar Nacion cewar masu cewar dan kwallon ya yi ritaya ba sa hangen annobar da Argentina za ta fada a fagen tamaula.

Maradona ya kara da cewar ya kamata Messi ya ci gaba da yi wa kasar wasa a gasar kofin duniya da za a yi a 2018, domin watakila Argentina ce za ta dauki kofin.

Messi ya lashe kofunan La Liga takwas da na zakarun Turai hudu a Barcelona.

Sai dai kuma babbar kyauta da ya ci wa kasar ita ce lambar Zinare a gasar Olympics da aka yi a 2008.