Sadio Mane ya koma Liverpool

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mane ya ce yana alfaharin komawa Liverpool

Kungiyar kwallon kafar Liverpool ta kammala sayen dan wasan Southampton Sadio Mane a kan £34m.

Dan wasan ya sanya hannu a kwantaragin shekara biyar, kuma shi ne dan wasa na uku da Liverpool ta saya a lokacin bazara bayan golan Jamus, Loris Karius da dan wasan baya na Kamaru, Joel Matip.

Za a iya kara kudin da aka sayi Mane, mai shekara 24, zuwa £36m inda zai haura kudin da Liverpool ta sayi dan wasan da ta saya mafi tsada Andy Carrol, a kan £35m a shekarar 2011.

Dan wasan ya zura kwallaye 21 a wasannin Premier 67 da ya buga wa kungiyar, bayan da ta saye shi daga Salzburg a shekarar 2014 a kan £10m.

Ya shaida wa shafin intanet na kungiyar cewa, "Yau babbar rana ce a wurina, kuma ina farin cikin zuwa daya daga cikin manyan kungiyoyin kwallon kafa a Turai. Wannan kungiya ce da ta dauki kofuna da dama, sannan ta kafa tarihi".