Ko ya dace a bar wa Yusuf Super Eagles?

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Nigeria za ta fafata da Kamaru da Algeria da Zambia

A karshen makon da ya wuce aka fitar da jadawalin wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya, bangaren nahiyar Afirka.

Hakan ne ya sa aka saka Nigeria da Kamaru da Algeria da kuma Zambia a cikin rukuni na biyu.

Salisu Yusuf ne ke jan ragamar Super Eagles a matsayin kociyan rikon-kwarya, tun bayan da kasar ta kasa samun gurbin shiga gasar nahiyar Afirka da za a yi a 2017.

Tun lokacin da aka ba shi aikin, ya jagoranci Nigeria ta doke Mali da Luxembourg a wasan sada zumunta.

Abin tambayar shi ne ko ya dace a bai wa Yusuf aikin jan ragamar tawagar kwallon kafa ta Nigeria, ko kuma a dauko koci daga waje.

Kociyan ya yi mataimaki karkashin Stephen Keshi da Shu'aibu Adamu da Sunday Oliseh da Samson Siasia.

Rasha ce za ta karbi bakuncin gasar cin kofin duniya da za a yi a 2018.