Neymar zai buga wa Brazil wasannin Olympics

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Brazil ce za ta karbi bakuncin wasannin Olympics da za a yi a bana

Neymar zai buga wa tawagar kwallon kafa ta Brazil tamaula, a gasar wasannin Olympics da za ta karbi bakunci ta bana.

Neymar mai murza-leda a Barcelona zai buga wa Brazil wasa ne a matsayin 'yan kwallo uku da suka haura shekaraun ka'ida a gasar.

Sauran 'yan wasa biyun da suka haura shekara 23 da za su wakilci Brazil a wasannin sun hada da Douglas Costa mai taka-leda a Bayern Munich.

Cikon na ukun shi ne mai tsaron ragar kungiyar Palmeiras, Fernando Prass.

Ga jerin 'yan wasan da za su wakilci Brazil a Olympics din:

Masu tsaron raga: Fernando Prass (Palmeira), Uilson (Atletico Mineiro).

Masu tsaron baya: Marquinhos (PSG), Luan (Vasco da Gama), Rodrigo Caio (Sao Paulo), Zeca (Santos), William (Internacional), Douglas Santos (Atletico Mineiro).

Masu buga tsakiya: Thiago Maia (Santos), Rodrigo Dourado (Internacional), Fred (Shakhtar Donetsk), Rafinha (Barcelona), Felipe Anderson (Lazio).

Masu cin kwallaye: Neymar (Barcelona), Douglas Costa (Bayern Munich), Gabriel Jesus (Palmeiras), Gabriel Barbosa (Santos), Luan (Gremio).