Nkoulou ya koma Lyon da taka-leda

Hakkin mallakar hoto olympic lyon
Image caption Nicolas Nkoulou dan wasan tawagar kwallon kafa ta Kamaru

Mai tsaron bayan tawagar kwallon kafa ta Kamaru, Nicolas Nkoulou, ya koma Lyon ta Faransa da murza-leda.

Nkoulou mai shekara 26, ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara hudu, bayan da kwantiraginsa ya kare da Marseille.

Shi kuwa dan wasan Najeriya, Dickson Nwakaeme, ya saka hannu kan yarjejeniya mai tsawo da kungiyar Angers.

Nwakaema mai shekara 30, ya koma Angers ne, bayan da ya buga wa kungiyar Pahang ta Malasiya wasanni shekara uku.