Man United ta kusa daukar Ibrahimovic

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ibrahimovic ya yi ritaya daga buga wa Sweden kwallon kafa

A karshen makon nan Manchester United za ta kammala daukar Zlatan Ibrahimovic domin ya buga wata tamaula.

Dan kwallon Sweden, mai shekara 34, wanda yarjejeniyarsa ta kare da Paris St-Germain a bana, ana sa ran zai buga wa United wasa shekara daya.

Ibrahimovic zai zama dan wasa na biyu da sabon koci Jose Mourinho ya dauko, tun da maye gurbin Louis van Gaal a watan Mayu.

Tun farko United ta dauki Erik Baily dan kasar Ivory Coast kan kudi fan miliyan 30 daga Villareal.

United din tana kuma yin zawarcin dan kwallon Borussia Dortmund, Henrikh Mkhitaryan domin ya koma Old Trafford da murza leda.