"Bilic ba zai zama kocin Ingila ba"

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Slaven Bilic zai ci gaba da jan ragamar West Ham a gasar Premier da za a yi.

Daya daga cikin mutanen da suka mallaki West Ham, David Gold, ya ce Slaven Bilic ba shi da sha'awar zama kocin Ingila.

Ingila ba ta da koci tunda Roy Hodgson ya yi ritaya daga aiki sakamakon doke su da Iceland ta yi 2-1 a gasar nahiyar Turai ranar Litinin.

Bilic, mai shekara 47, ya jogoranci West Ham ta kare a mataki na bakwai a kan teburin gasar Premier da ta kammala.

Ana rade-radin kocin, wanda ya horar da tawagar Croatia daga 2006 zuwa 2012, zai maye gurbin Roy Hodgson.

Bilic ya ci Ingila a watan Nuwamba a shekarar 2007, lokacin da Croatia ta doke fitar da kasar daga wasan neman gurbin shiga gasar nahiyar Turai ta 2008.

Haka ne ya sa Ingila ta kori Steve McClaren daga aikin horar da tawagar ta Ingila.