Neymar zai ci gaba da wasa a Barca - Bartomeu

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Neymar zai buga wa Brazil tamaula a wasannin Olympic

Neymar zai ci gaba da buga tamaula a Barcelona, kuma yana daf da sanya hannu kan yarjejeniyar tsawaita zamansa a kungiyar, in ji shugaban kungiyar Josep Bartomeu.

Neymar, mai shekara 24, ya ci kwallaye 55 a wasannin La Liga 93 da ya buga wa Barcelona tun lokacin da ya koma can da taka leda.

Barcelona ta sayi dan wasan na tawagar Brazil daga Santos a shekarar 2013 a kan fan miliyan 48 da 60000

Wasu rahotanni na cewar Manchester United da Paris Saint Germain suna zawarcin dan kwallon, wanda yarjejeniyarsa da Barca za ta kare a 2018.

Bartomeu ya ce "Neymar na son ya ci gaba da zama a Barcelona, kuma mun kusa cimma yarjeniyar da dan wasan".

Neymar ya kuma ci wa tawagar kwallon kafa ta Brazil 46 daga wasanni 70 da ya buga mata.