Potugal ta kai wasan daf da karshe a kofin Turai

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Karo na hudu kenan Portugal na kaiwa wasan daf da karshe a gasa biyar baya da ta buga

Portugal ta kai wasan daf da karshe a gasar kofin nahiyar Turai, bayan da ta ci Poland 5-3 a bugun fenariti.

Kasashen sun tashi wasa kunnen doki 1-1 a minti 120 da suka kara har da karin lokaci.

Poland ce ta fara cin kwallo ta hannun Robert Lewandowski a minti na biyu da take leda.

Portugal ta farke a minti na 33 ana tsaka da wasa ta hannun Renato Sanches.

Wannan shi ne karo na hudu a jere da Portugal ke kaiwa wasan daf da karshe a gasar ta Turai, daga biyar da ta je a baya-bayan nan.