An tuhumi likita da kashe Ekeng da gangan

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A cikin watan Mayu Elena Duta ya fadi a cikin filin wasa lokacin yana buga gasar Romania

Mai shigar da kara a Romania ya tuhumi likita Elena Duta, da kashe dan kwallon Kamaru, Patrick Ekeng da gangan.

Ekeng mai shekara 26, ya fadi a cikin filin wasa a lokacin da yake tsaka da buga wa Dinamo Bucharest kwallo.

Lamarin ya faru ne a cikin watan Mayu bayan da zuciyarsa ta daina buga wa a lokacin da yake taka leda a gasar ta Romania.

Mai shigar da karar ya ce Dakta Duta, wadda ta kware a aikin bayar da agajin gaggawa ba ta taimaka wa dan wasan ba, a lokacin da za a kai shi asibiti a motar daukar marasa lafiya.

Lokacin da aka kai dan kwallon asibiti likitoci sun kasa farfado da Ekeng.

A gwaje-gwajen da aka yi an ce dan wasan ya mutu ne sakamakon bugun zuciya mai tsanani da ya yi fama da shi.

Mai shigar da karar ya ce ko da zuciyarsa ce ta daina buga wa da likitan ta yi iya kokarinta da ta ceci ran dan wasan.

Ya kuma kara da cewar ba ta gwada yanayin da Ekeng ya shiga ba, kuma ba ta yi kokarin ceto ransa ba.