Crystal Palace ta sayi Townsend

Hakkin mallakar hoto All Sport

Kungiyar kwallon kafar Crystal Palace ta sayi dan wasan tsakiya Andros Townsend daga Newcastle a kan £13m wanda zai yi shekara biyar.

Dan wasan mai shekara 24 dan kasar Ingila ya kammala sanya hannu kan yarjejeniyar komawa Palace ne a daidai lokacin da dan wasan Palace Dwight Gayle shi kuma zai koma Newcastle.

Townsend ya zura kwallo sau hudu a wasanni 13 da ya buga wa Newcastle, bayan da ya koma can daga Tottenham a watan Janairu a kan £12m.

Dan wasan ya ce: "Na yi matukar jin dadin komowa ta Crystal Palace domin taka muhimmiyar rawa."