Chelsea ta dauki Batshuayi daga Marseille

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Michy Batshuayi ya koma Marseille da wasa ne a shekarar 2014

Chelsea ta sanar da kammala daukar dan kwallon Marseille, Michy Batshuayi kan yarjejeniyar shekara biyar.

Dan kwallon zai buga tamaula a Stamford Bridge kan kudi fam miliyan 33 da dubu 200, bayan da ya taka-leda na shekara biyu a Marseille.

Batshuayi ya fara buga tamaula a Standard Li├Ęge daga nan ne ya koma Marseille da wasa a shekarar 2014.

A kakar farko da ya fara yi wa Marseille wasanni, ya ci mata kwallaye 15, a kuma gasar da aka kammala ta bana ya zura kwallaye 17 a raga.

Hakan ne ya sa tawagar Belgium ta gayyace shi wasannin gasar cin kofin nahiyar Turai, ya kuma ci kwallo a wasan da suka ci Hungary 4-0.