Leicester City ta dauki Nampalys Mendy

Image caption Nampalys Mendy ya koma Leicester City da taka leda

Leicester City ta dauki Nampalys Mendy daga kungiyar Nice ta Faransa, kan yarjejeniyar shekara hudu.

Dan wasan mai shekara 24, ya buga tamaula karkashin koci Claudio Ranieri wanda ya horar da Monaco a baya, yanzu yake jan ragamar Leicester City.

Daga baya ne Mendy ya koma murza-leda a Nice a shekarar 2013, inda ya buga mata wasannin League sau 100.

Dan kwallon ya buga wa tawagar Faransa ta matasa ‘yan kasa da shekara 21 wasanni biyar, amma har yanzu ba a gayyace shi zuwa babbar tawagar kasar ba.