Man City na son sayen John Stone

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Everton bata son sayar da John Stone

Manchester City na son ta sayi dan kwallon Everton, John Stone, mai tsaron bayan tawagar Ingila.

Sai dai kuma Everton ta bukaci City ta biya fam miliyan 50, idan har tana son ya koma Ettihad da murza-leda.

Har yanzu kungiyoyin biyu ba su zauna taro don cimma matsaya a kan Stone din ba, idan suka kulla ciniki a hakan, zai zama dan wasan Biritaniya mafi tsada a tarihi.

Everton dai ba ta son ta sayar da mai tsaron bayan, amma tana jin tsoron kar a yi mata sakiyar da ba ruwa, ya yanke komawa wata kungiyar da kansa.

A bara ma Everton ba ta amince da tayin da Chelsea ta yi wa dan kwallon kan kudi fam miliyan 40, karkashin koci Jose Mourinho ba.