Federer ya kai wasan daf da na kusa da karshe

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Federer ya kai zagayen gaba ne bayan ya doke Marin Cilic

Zakaran gasar tennis karo bakwai, Roger Federer ya kai wasan daf da na kusa da karshe a gasar kwallon tennis ta Wimbledon.

Federer ya kai wasan zagaye na gaba a gasar ne, bayan da ya doke Steve Johnson da ci 6-2 6-3 7-5.

Da wannan nasarar da Federer ya samu, zai kara da Marin Cilic a wasan daf da na kusa da karshe..

Johnson yana samun horo ne tare da koci daya da Sam Querrey wanda ya fitar da Novak Djokovic a wasan zagaye na uku a gasar ta Wimbledon.