An fitar da jadawalin gasar kwallon rairayi ta Afirka

Hakkin mallakar hoto no credit
Image caption Hukumar CAF ce ta fitar da jadawalin gasar

Hukumar kwallon kafa ta Afirka, CAF, ta raba jadawalin kasashe 14 da za su buga wasannin share fagen shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka ta kwallon rairayi.

Kasashen da za su fafata a wasannin sun hada da tsibirin Cape Verde da Cote d’Ivoire da Ghana da Masar da Liberia da Libya da Kenya da Madagascar da Morocco da Mozambique da Senegal da Sudan da Tanzania da kuma Uganda.

Daga cikin kasashen ne, za a fitar da zakaru bakwai da za a hada su da mai masaukin baki Nigeria, domin fafatawa a gasar kwallon rairayi ta Afirka ta bana daga tsakanin 13–18 ga watan Disambar 2016.

Bayan kammala gasar, dukkan kasashe biyu da suka kai wasan karshe, sune za su wakilci Afirka a gasar kwallon rairayi ta duniya da za a yi tsakanin 27 ga watan Afirilu zuwa 7 ga watan Mayun 2017 da za a yi a Bahamas.

Tawagar Madagascar ce ta lashe gasar nahiyar Afirka da aka yi a shekarar 2015, inda ta doke Senegal da ci 2-1 a bugun fenariti da za su kara a Seychelles.