Torres ya tsawaita zamansa a Atletico Madrid

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Torres ba zai bar Atletico Madrid ba

Dan kwallon Atletico Madrid, Fernando Torres, ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da buga tamaula a kungiyar.

Torres dan wasan tawagar Spaniya, ya amince zai ci gaba da murza-leda zuwa shekara daya, bayan da yarjejeniyar da ya kulla a baya ta kare a makon jiya.

Dan wasan mai shekara 32, tsohon dan kwallon Liverpool da Chelsea, ya koma Atletico, wacce ya fara yi wa wasa a kwararren dan kwallo daga AC Milan a shekarar 2015.

Torres ya ci kwallaye 12 a wasanni 44 da ya buga wa Atletico a kakar wasannin da aka kammala, kuma kungiyar ta yi rashin nasara a hannun Real Madrid a gasar cin kofin zakarun Turai a was an karshe.

Shi ma dan kwallon tawagar Faransa dake buga gasar nahiyar Turai, Antoine Griezmann, ya tsawaita zamansa a makon jiya.