An kafa damben da za a ci mota a Kano

Image caption Za a bai wa wanda ya lashe gasar kyuatra motar hawa

Kungiyar wasan damben gargajiya ta jihar Kano, ta saka gasar da za a ci mota a lokutan da za a yi bukukuwan karamar Sallah ta bana.

Kungiyar ta tsayar da ranar Juma’a 8 zuwa 15 ga watan Yuli, domin fitar da zakaran damben gargajiya da za ta ba shi motar hawa .

Shugaban kungiyar Mamman Bashar da ake kira Danliti, ya ce sun yi shirin hakan ne da nufin zaburar da 'yan wasan dambe da kuma daga martabarsa a idanun duniya.

Ya kuma ce a lokacin gasar sun tsara dokokin da za a fitar da zakaran da zai lashe kyautar, wanda suka gayyato fitattun ‘yan damben gargajiya da ke fadin kasar.

Haka kuma da zarar an sanar da ranar da za a yi karamar sallar, kungiyar za ta fara yin wasannin damben gargajiya kafin a fara gasar da za a lashe kyautar motar hawa.

Bayan da kungiyar ta shirya bayar da mota ga wanda ya zama zakara a gasar, za kuma ta bai wa na biyu kyautar babur din hawa, na uku kuma zai samu kudi naira dubu 50.

Za a yi wasannin ne a gidan damben gargajiya na Ado Bayero Square da ke jihar Kano a Nigeria.