Wimbledon: Venus ta kai wasan daf da karshe

Hakkin mallakar hoto
Image caption Venus Williams ta kai wasan daf da karshe a gasar Wimbledon

Venus Williams ta kai wasan daf da karshe a gasar kwallon tennis ta Wimbledon, wacce rabon da ta yi hakan tun a shekarar 2009.

Venus din ta kai wasan zagayen daf da karshe ne, bayan da ta doke Yaroslava Shvedova da ci 7-6 (7-5) 6-3.

‘Yar wasan za ta buga karawar gaba ne da Angelique Kerber, wacce ta casa Simona Halep da ci 7-5 7-6 (7-2).

Venus ta lashe manyna gasar kwallon tennis sau biyar a tarihi.