Schweinsteiger zai buga karawa da Faransa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kyaftin na tawagar Jamus a gasar Euro2016, Bastian Schweinsteiger

Bastian Schweinsteiger ne zai jagoranci tawagar Jamus a matsayin Kyaftin dinta a fafatawar da za ta yi da Faransa a ranar Alhamis in ji koci Joachim Low.

Kasashen biyu za su kara ne a wasan daf da karshe a gasar cin kofin nahiyar Turai da Faransa ke karba bakunci a birnin Marseille.

Dan kwallon mai taka leda a Manchester United, mai shekara 31, yana jinyar rauni a gwiwarsa, wanda ake tantama idan zai iya buga fafatawar.

Kociyan tawagar Jamus, Low ya ce yana cikin matsin ‘yan wasan da zai zaba su fuskanci Faransa, amma yana da tabbacin cewar da Schweinsteiger za a fara wasan,

Haka kuma kocin zai nemi ‘yan kwallon da za su maye gurbin Khedira da Gomez wadanda suka yi rauni, da kuma Hummels wanda ba zai buga wasa daya ba, sakamakon katin gargadi da ya karbi guda biyu.