Leicester ta sayi Ahmed Musa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ahmed Musa ne dan wasa mafi tsada da Leicester ta taba saya

Leicester City, wacce ta lashe kofin Premier na bana, ta kammala sayen Ahmed Musa daga CSKA Moscow kan fan miliyan 16.

Ahmed Musa shi ne dan kwallo na farko da kungiyar ta saya mafi tsada a tarihi, tun lokacin da aka kafa ta shekara 132 da suka wuce.

Dan wasan tawagar kwallon kafar Nigeria, mai shekara 23, ya koma CSKA Moscow a shekarar 2012, ya kuma ci kwallaye 54 daga wasanni 168 da ya buga mata tamaula.

Musa shi ne dan kwallo na hudu da Leicester ta saya a bana, da suka hada da mai tsaron raga Ron-Robert Zieler da mai tsaron baya Luis Hernandez da mai wasan tsakiya Nampalys Mendy.

CSKA Moscow ce ta lashe kofin gasar kasar, inda Musa ya fara buga mata wasanni a shekarar 2012 ya ci mata kwallaye 54 daga wasanni 168 da ya yi