Bielsa ya ajiye aikin horar da Lazio

Hakkin mallakar hoto EPA

Tsohon kociyan tawagar kwallon kafa ta Argentina, Marcelo Bielsa, ya ajiye aikin horar da Lazio kwana biyu da karbar matsayin.

A ranar Laraba ne Lazio ta sanar da nada Bielsa, mai shekara 60, a matsayin kociyanta domin ya maye gurbin Stefano Pioli, wanda ta kora a watan Afirilu.

A kuma ranar Juma’a ne Roma ta sanar da cewar Bielsa ya rubuta takardar ajiye aiki.

Rabon da Lazio ta dauki gasar Serie A ta Italiya tun a shekarar 2000, kuma a mataki na takwas ta kare a gasar da aka kammala.