Cech ya daina buga wa kasarsa tamaula

Hakkin mallakar hoto Reuters

Golan Arsenal, Petr Cech, ya ce ba zai sake buga wa kasarsa Jamhuriyar Czech kwallon kafa ba.

Cech, mai shekara 34, ya fara buga wa tawagar kwallon kafa ta Jamhuriyar Czech wasa a shekarar 2002, ya kuma murza mata leda sau 121.

Mai tsaron ragar yana daga cikin tawagar da Jamhuriyar Czech da ta kai wasan karshe a gasar kofin nahiyar Turai da Girka ta doke su a shekarar 2004.

Cech ya koma Arsenal da murza-leda daga Chelsea a shekarar 2015.