Barca ta bukaci a marawa Messi baya

Image caption Kotun Spaniya ta yankewa Messi daurin wata 21

Barcelona ta fara gangamin a marawa Lionel Messi baya, bayan da wata kotu ta same shi da laifin kin biyan kudin haraji.

Kotun ta Spaniya ta yankewa Messi da kuma mahaifinsa hukuncin zaman gidan yari watanni 21.

Sai dai kuma sun ce za su daukaka kara, kan samunsu da laifin kin biyan harajin da suka kai kudi Yuro miliyan hudu da dubu dari daya daga tsakanin shekarar 2007 zuwa 2009 da aka yi.

Ba a dai tsammanin dan kwallon da kuma mahaifinsa za su zauna a gidan wakafi, sai dai kuma Barcelona ta fara kamfen a kafar sada zumunta cewar ya kamata a marawa Messi baya dari bisa dari.

Haka kuma kotun ta ci tarar Messi kudi Yuro miliyan biyu, yayin da mahaifinsa zai biya tarar kudi Yuro miliyan daya da dubu dari biyar.