An raba jadawalin damben Mota

Image caption Wannan ita ce motar da aka saka da za a ci a gasar

An raba jadawalin da ‘yan wasan damben gargajiya za su fafata a tsakaninsu, domin lashe kyautar motar hawa a ranar Lahadi a gidan damben Ado Bayero Square da ke birnin Kano.

An zabo ‘yan wasa guda shida daga bangaren Guramada da guda shida daga Arewa da kuma guda shida da suke kare martabar Kudu.

Cikin sharudan wasan da za a fafata, duk dan damben da aka kira shi bai fito fili ba, to abokin karawarsa ya kai zagayen gaba kenan a gasar.

Haka kuma akwai bayar da maki ga dan wasa, ko gargadi ga wanda ya yi laifi, domin idan suka yi turmi uku babu kisa, ta haka za a yi lissafin da dan dambe zai kai wasan zagayen gaba.

Za a fara wasannin ne da yammacin Lahadi, kuma ana sa ran za a yi mako guda ana yin gumurzu.

Ga yadda aka raba jadawalin wasannin:

1. Shagon Shaf-Shaf Guramada da Shagon Mada daga Kudu

2. Cikan Guramada da Bahagon Sanin Kurna daga Arewa

3. Garkuwan Ali Fada Guramada da Dan Inda daga Arewa

4. Dogon Kyallu Guramada da Ebola daga Kudu

5. Habu Bahago Guramada da Shagon Bahagon Sarka daga Kudu

6. Dogo Mai Takwasara Guramada da Shagon Tuwo daga Arewa

7. Shagon Aleka daga Kudu da Dogon Bunza Arewa

8. Dan Sama'ila da Shagon Buhari daga Arewa

9. Bahagon Mai Maciji da Shagon Sawun Kura daga Arewa