Man United ba ta dokin ta dauki Pogba

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Man U ta ce ba ta gaggawar sayen Pogba

Manchester United tana sha’awar ta sake dauko Paul Pogba ya buga mata tamaula a Old Trafford, amma ba ta gaggawar sai lallai ta sayi dan kwallon.

Ana ta rade-radin cewar United ta biya kudin dan wasan da suka kai fam miliyan 100, sai dai kuma an shaida wa BBC cewar babu wata yarjejeniya da aka cimma.

Hasali ma United ba ta tuntubi Juventus kan batun a sayar mata da dan kwallon tawagar Faransan ba.

Har yanzu Juventus ba ta ce uffan ba dangane da batutuwan da ake yi kan komawar Pogba United da murza leda, wanda yarjejeniyarsa za ta kare a Juventus a shekarar 2019.