Wakaso ya koma Panathinaikos da taka-leda

Hakkin mallakar hoto
Image caption Wakaso ya bar Rubin Kazan

Dan kwallon tawagar Ghana, Mubarak Wakaso, ya koma kungiyar Panathinaikos ta Girka da taka-leda daga Rubin Kazan ta Rasha.

Tuni kuma dan wasan mai shekara 25, ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara uku.

Wakaso ya fara tamaula a Rubin Kazan tun cikin shekarar 2013, sai dai ya buga wasanni ne aro a Celtic da kuma Las Palmas.

Dan wasan ya taimakawa Ghana kai wa karawar gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a yi a Gabon a shekarar 2017, da kuma wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya.