Ba a tuntubi Allardyce kan horar da Ingila ba

Hakkin mallakar hoto z
Image caption A wannan makon ne hukumar kwallon kafar Ingila za ta gana da Allardyce

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ba ta tuntubi kociyan Sunderland, Sam Allardyce domin bashi aikin horar da tawagar kwallon kafa ta Ingila ba.

An ruwaito cewar a makon nan ne hukumar kwallon kafa ta Ingila za ta gana da Allardyce, domin maye gurbin Roy Hodgson wanda ya yi murabus, bayan da aka fitar da Ingila daga gasar Turai ta Faransa.

Allardyce mai shekara 61, yana tare da kungiyar Sunderland a Austria, inda suke yin atisayen tunkarar wasannin kakar bana.

An kuma alakanta cewar kociyan tawagar Amurka, Jurgen Klinsmann da na Bournemouth Eddie Howe, da aikin horar da Ingila.