Za a cigaba da gasar Federation Cup ta Nigeria

A ranar Talata za a ci gaba da gasar kwallon kafa ta cin kofin kalubale ta Nigeria da ake kira Confederation cup wasannin daf da na kusa da karshe.

Wasannin da za a fara daga ranar 12 zuwa 13 ga watan Yuli, zai kunshi karawa a wasannin maza da kuma na mata.

An kuma tsayar da ranar 13 ga watan Yuli domin fafatawa a kwantan wasa tsakanin Enyimba da kuma El-Kanemi Warriors a Abuja, duk wacce ta samu nasara za ta yi gumurzu ne da J. Atete FC da za a sanar da ranar wasan a nan gaba.

Ga jadawalin fafatawar maza da ta mata da wurin da za a yi wasannin:

Wasannin Maza ranar Talata

Akwa United Vs Sunshine Stars - Makurdi

Crown FC Vs Enugu Rangers - Kaduna

Wasannin maza ranar Laraba

Rivers United Vs Shooting Stars - Kaduna

Wikki Tourists Vs Plateau United - Akure

Katsina United Vs FC IfeanyiUbah - Ilorin

Prime FC Vs Warri Wolves - Makurdi

Dynamite FC Vs Nasarawa United - Lokoja

Wasannin mata ranar Talata

Nasarawa Amazons Vs Abia Angels - Lokoja

Delta Queens Vs Katsina Queens - Abuja

Wasannin mata ranar Laraba

COD United Vs Bayelsa Queens - Lokoja

Sunshine Queens Vs Rivers Angels - Abuja