Watakila Murray ba zai buga Davis Cup ba

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A ranar Lahadi ne Murray ya lashe gasar Wimbledon karo na biyu

Andy Murray ya ce da kyar idan zai buga wa Birtaniya wasan daf da na kusa da karshe a gasar tennis ta Devis Cup da za su fafata da Serbia a karshen makon nan.

Murray ya lashe kofin gasar Wimbledon karo na biyu a ranar Lahadi, bayan da ya doke Milos Raonic a wasan karshe.

Murray din ya ce zai bayyana matsaya, idan ya kammala tattaunawa da kyaftin din tawagar Birtaniya Leon Smith.

Tuni kuma Novak Djokovic wanda ke mataki na daya a jerin wadanda suka fi iya kwallon tennis a duniya ya fice daga tawagar Serbia.

Murray zai bi tawagar Birtaniya a karawar da za ta yi a Belgrade ko da ba zai buga mata wasan ba, domin ya ce zai iya kara musu kwarin gwiwa a lokacin fafatawar.