Sharapova ba za ta je wasannin Olympic ba

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sharapova ba za ta je Olympic ba

Maria Sharapova ba za ta halarci gasar kwallon tennis da za a yi a wasannin Olympic da Brazil za ta karbi bakunci ba.

Hakan ya biyo bayan da kotun daukaka kararrakin wasanni ta duniya ta ce ba za ta fara sauraren karar da Sharapova ta shigar ba, har sai a cikin watan Satumba.

An dakatar da ‘yar wasan wacce ta lashe manyan gasar tennis biyar daga shiga wasannin tsawon shekara biyu, bayan da aka sameta da laifin amfani da kwayar Meldonium wacce aka hana ‘yan wasa su sha.

Sharapova wacce ta daukaka kara da kuma hukumar wasan kwallon tennis ta duniya suna bukatar lokaci, domin su kimtsa kafin a fara sauraren daukak karar.

A ranar 19 ga watan Satumba ne ake sa ran yanke hukunci.

Za a fara gasar wasannin Olympic da Brazil za ta karbi bakunci daga ranar 5 ga watan Agustan 2016.