An kashe jami'an kwallon Sudan ta Kudu

South Sudan Hakkin mallakar hoto other
Image caption Atlabara ne zakarun Premier a Sudan ta Kudu

An kashe jami'ai biyu na kulob din Atlabara na Sudan ta Kudu a rikicin baya-bayan nan da ya barke a kasar.

William Batista, sakatare janar na kungiyar, wacce ita ce mai rike da kanbun gasar Premier ta kasar, da Leko Nelson, manajan kulob din, an kashe su ne a karshen makon da ya gabata.

Shugaban hukumar kwallon kafa ta kasar Chabur Goc ne ya sanar da rasuwar mutanen biyu a ranar Lahadi da daddare.

Dakarun da ke biyayya ga Shugaba Salva Kiir da na Mataimakinsa Riek Machar sun fara kaiwa juna hari a kan titunan Juba a makon da ya gabata.